Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta
maku bisa nakaltowa daga shafin watsa labarai na Quds
cewa: Ministan harkokin wajen na Amurka ya yi iƙirari: “Wannan wani muhimmin
lokaci ne. Wataƙila ita ce mafi kyau dama ta ƙarshe don dawo da fursunonin
gida, da gudanar da tsagaita wuta da sanya kowa a kan kyakkyawar turba don
wanzar da zaman lafiya da tsaro".
Ministan harkokin wajen Amurka ya isa birnin Tel Aviv a daren jiya da nufin tattauna shawarwarin tsagaita wuta a Gaza.
Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya sanar da cewa, Blinken zai kuma gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ziyararsa ta goma a yankunan da aka mamaye tun farkon yakin Gaza.
Bayan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, sakataren harkokin wajen Amurka zai je Masar domin tattaunawa da mahukuntan kasar da ke shiga tsakani a tattaunawar.